'Abin da ya sa nake tsoron soyayya a matsayi na na wada'

Pani Mamuneas

Asalin hoton, CHANNEL 4

Bayanan hoto,

Pani Mamuneas dan wasa ne kuma yana karatun digiri a fannin shari'a

Dan wasan guje-guje kuma dalibin shari'a, Pani Mamuneas, bai taba yin budurwa ba, kuma yana tunanin cewa matan da suke kusantarsa suna son wada ya kasance cikin jerin wadanda suka taba soyayya da su ne kawai.

Dan shekara 19 ya yanke shawara yin wani abu game da shi kuma ya nemi shiga wani shirin soyayyar talabijin.

Ko da yaushe za ka ji 'yan mata suna cewa " wanne iri ne naka? Mai tsayi, kasan mai tsayi da kyau, kuma ni akasin hakan ne.

A tsayin kafa hudu da inci bakwai mutane suna tambaya na 'shin za ka so ace an haife ka da tsayi?' Amma yanzu ba zan iya tunanin rayuwa ta wani yanayi na daban ba.

A lokacin da nake yaro, ban ga kaina a matsayin wani mai nakasa ba. Kai ba na ma lura da shi, har sai da na kai shekara sha wani abu a lokacin da wasu suka fara girma kuma na fara ganin na fita daban kuma makaranta ta yi mun wahala.

'Yan uwana dalibai a makaranta a Leicester za su tambaye ni 'pani ya ya kake dan karami ne? An haife ka kamar kwayan wake ne?' A yanzu idan na yi tunani kan abinda ya faru a baya, a iya kauce wa abubuwan da suka bata mun rai cikin sauki in gane cewa mutane suna so su sani ne- yara ne wadanda suke tambayoyi marasa ma'ana. Ina da wata larurur wadanni wadda ake cewa Achondroplasia.

Asalin hoton, CHANNEL 4

Bayanan hoto,

Pani Mamuneas ya gane larurarsa ne a lokacin da ya ga sa'o'insa sun zarce shi a girma

A zahiri na fi yawancin wadanda suke da irin larurata, amma ni karami ne kuma ya yi tasiri kan dangantakata da kuma yadda nake ganin kai na a shekarun baya.

Ni da abokai na muna hira kan 'yan mata da kuma mashahuran mutane, wadanda muke sa ran zamu aure da kuma yadda za mu neme su da aure.

A lokcin da nake shekara 12 na nemi wata yarinya. Mun je sinima, kuma kamar mun ji dadi, amma washe gari sai gulma ta fara.

Na shaida wa wani aboki na a dakin karatun makaranta cewa ina son ta, amma sai ya rubuta a manyyan harrufa a kan allo domin kowa ya gani. Da na gani, sai naji kamar na bace daga doron kasa.

Ni da yarinyar mun yi hawaye kuma ta ji kunya sosai ta yadda ba ta sake mun magana ba.

A lokacin ne na rasa karfin gwiwa na, kuma na yi tunanin cewar ina da nakasa saboda tsawo na.

Na daina magana da 'yan mata kuma ba zan bayyana ba idan ina kaunar mace.

Ina tsoron abinda 'yan mata za su yi tunani game da ni, ina fargabar cewar za su iya kin kula ni ko su tsokane ni ko kuma su kalle ni a matsayin ni ba kowa ba ne domin na fita daban.

Ya kasance wani mawuyacin lokaci a rayuwata.

Asalin hoton, CHANNEL 4

Bayanan hoto,

Yanzu Pani Mamuneas yana farin ciki da irin halittarsa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Pani Mamuneas

Da na shiga jami'a abubuwa suka fara canzawa. Kowa ya mallaki hankalinshi kuma musgunawa ta tsaya. Sai naga lokaci yayi da ya kamata na gane ko ni wanene da kuma abin da nake so na yi nan gaba.

A wannan lokacin ne kasancewar wanda bai taba samun budurwa ba na yanke shawara na tuntubi gidan na channel 4 inda ake shirin Undateables, shiri ne da ke hada masu nakasa da wandanda za su aura. Saboda haka na yanke shawarar kawar da tsoron soyayya na shiga shirin da fatan samun wadda zan aura.

Abu ne mai wuya, amma na yi tunanin in zan iya fara soyayya kan shirin talabijin ba zan samu wata matsalar kwarin guiwa ba nan gaba.

Shiga shirin ya taimaka min kuma yanzu ina iya tunkarar mace in yi mata magana domin na koyi cewa babu abinda ya kamata naji tsoro. Idan macen ba ta so na, babu wata matsala. Wasu masu kyakyawar niya bani hadin kai.

Na kasance cikin wasannin kasa-da-kasa kuma na yi fatan shiga gasar paralympic wadda aka yi a Rio a bara, amma ciwo ya hana ni.

Shiga shirin Undateables ya taimaka min wajen mayar da hankali na kan wani bangaren rayuwa daban kuma ya dauke tunani na daga nakasata duk da cewa yanzu na koma atisaye da nufin shiga gasar Paralympics na shekarar 2020 a Tokyo da kuma yin karatun digiri a fannin shari'a.