Ronaldo ne gwarzon dan kwallon kafa na Fifa na 2016

Fifa Award

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo ne gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2016

An bayyana sunan Cristiano Ronaldo a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya, na Fifa na shekarar 2016.

Ronaldo ya yi nasara ne a kan Lionel Messi na Barcelona da Antone Griezmann na Atletico Madrid.

A watan jiya ne Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d'Or wadda mujallar Faransa ke gudanarwa kuma karo na hudu da ya lashe ta.

Ronaldo, ya lashe kofin nahiyar Turai tare da Portugal a 2016, ya kuma ci kofin zakarun Turai da na zakarun nahiyoyin duniya tare da Real Madrid.