Manchester United za ta karbi bakuncin Wigan a gasar kofin FA

English FA

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United ce ke rike da kofin FA wanda ta lashe a bara

Mai rike da kofin FA, Manchester United za ta karbi bakuncin Wigan Athletic a wasannin zagaye na hudu a gasar cin kofin kalubalen Ingila.

Mai rike da kofin Premier na bara Leicester City za ta ziyarci Derby County, yayin da Chelsea da Brentford za su kece raini a wasan hamayya na kungiyoyin da ke arewacin Landan.

Milwall mai buga karamar gasar Ingila wadda ta fitar da Bournemouth daga wasannin, za ta kara a gida da Watford mai buga gasar Premier.

Za a fara wasannin zagaye na hudu a gasar da za ta kunshi kungiyoyi 32 da za su rage a gasar cin kofin FA da za a fara a ranar 27 zuwa 30 ga watan Janairun 2017.

Ga jadawalin wasannin da za a yi:

 • Tottenham Hotspur v Wycombe Wanderers
 • Derby County v Leicester City
 • Oxford United v Newcastle United or Birmingham City
 • AFC Wimbledon or Sutton United v Cambridge United or Leeds United
 • Plymouth Argyle or Liverpool v Wolverhampton Wanderers
 • Southampton or Norwich City v Arsenal
 • Lincoln or Ipswich v Brighton
 • Chelsea v Brentford
 • Manchester United v Wigan Athletic
 • Millwall v Watford
 • Rochdale v Huddersfield Town
 • Burnley or Sunderland v Fleetwood Town or Bristol City
 • Blackburn Rovers v Barnsley or Blackpool
 • Fulham v Hull City
 • Middlesbrough v Accrington Stanley
 • Crystal Palace or Bolton v Manchester City