Chelsea ta daukaka kara kan jan katin da aka bai wa John Terry

fa Cup
Bayanan hoto,

A ranar Lahadi ne Chelsea ta kai wasan zagaye na hudu a gasar cin kofin FA

Chelsea ta daukaka kara kan korar kyaftin din ta John Terry da aka yi a wasan cin kofin FA a karawar da ta samu nasara a kan Peterborough a ranar Lahadi.

Alkalin wasan Kevin Friend ne ya bai wa Terry jan kati, bayan da ya yi wa Lee Angol keta, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a karawar da Chelsea ta ci Peterborough 4-1.

A ranar Talata ake sa ran hukumar kwallon kafa ta Ingila za ta saurari korafin da Chelsea ta shigar mata.

Idan har hukumar ba ta soke hukuncin da aka yi wa Terry ba, to ba zai buga wasa da Chelsea za ta yi da Leicester City a gasar Premier a ranar Asabar ba.

Karawar da Terry ya buga wa Chelsea a ranar Lahadi ita ce ta farko wanda rabon da ya taka-leda tun cikin watan Oktoban da ya wuce.