Kididdigar bajintar da Ronaldo ya yi a tamaula

Fifa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo ne gwarzon kwallon kafa na Fifa na 2016

A ranar Litini Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2016 da hukumar Fifa ta karrama.

Dan wasan mai shekara 31, ya yi nasara ne a kan Lionel Messi da Antoine Griezmann, kuma a cikin watan Disambar 2016 ne ya lashe kyautar Ballon d'Or.

Ga kididdigar bajintar da Ronaldo kyaftin din tawagar Portugal mai taka-leda a Real Madrid ya yi:

55 - Kwallayen da ya ci a shekarar 2016 (42 a Real Madrid da guda 13 da ya ci wa Portugal)

4 - Yawan kyautar Ballon d'Or da ya lashe a 2008 da 2013 da 2014 da kuma 2016.

136 - Yawan wasannin da ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Portugal.

68 - Yawan kwallayen da ya ci wa kasarsa a fagen tamaula.

4 - Ronaldo shi ne dan wasa na farko da ya ci kwallaye a gasar cin kofin nahiyar Turai hudu dabam-dabam (2004 da 2008 da 2012 da kuma 2016).

80 - Fam miliyan 80 Real Madrid ta bai wa Manchester United a shekarar 2009 kan daukar Ronaldo.

17 - Kwallayen da ya zura a raga a a kakar wasa guda a gasar cin kofin zakarun Turai ta 2014.

9 - Kwallayen da ya ci jumulla a gasar cin kofin nahiyar Turai, wanda ya yi kan-kan-kan da Michel Platini.

381 - Yawan kwallayen da Ronaldo ya ci wa Real Madrid a wasanni 368 da ya buga mata.

14.1 - Sama da fam miliyan 14 da yake karba kudin takalmin da yake saka wa kamfanin Nike.

49,320,754 - Yawan mutanen da suke bibiyarsa a Twitter.

118,930,492 - Masu bibiyarsa a Facebook.