John Terry ba zai buga wa Chelsea wasa daya ba

FA cUP
Bayanan hoto,

Terry ba zai buga wa Chelsea karawar da za ta yi da Leicester ba a gasar Premier ranar Asabar

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta kori karar da Chelsea ta shigar kan jan katin da aka bai wa kyaftin dinta John Terry a ranar Lahadi a wasan kofin FA.

Alkalin wasan Kevin Friend ne ya bai wa Terry jan kati, bayan da ya yi wa Lee Angol keta, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a karawar da Chelsea ta ci Peterborough 4-1.

Da wannan mataki da hukumar kwallon Ingila ta dauka na nufin Terry ba zai buga wasa da Chelsea za ta yi da Leicester City a gasar Premier a ranar Asabar ba.

Karawar da Terry ya buga wa Chelsea a ranar Lahadi ita ce ta farko, wanda rabon da ya taka-leda tun cikin watan Oktoban da ya wuce.