Arsenal ta dauki matashin dan wasa Bramall

Arsenal
Bayanan hoto,

A karshen kakar bana yarjejeniyar Wenger za ta kare a Arsenal

Arsenal ta sanar da daukar matashin dan kwallo mai tsaron baya, Cohen Bramall, daga Hednesford Town.

A makon jiya dan kwallon ya yi atisaye da Gunners, kuma nan da nan aka amince ya fara buga tamaula a karamar kungiyar Arsenal ta matasa masu shekara 23.

Dan wasan mai shekara 20 wanda ke yin aiki a kamfanin hada motoci na Bentey, ya buga wa Hednesford Town wasanni na wucin gadi.

A watan jiya kungiyar ta Hednesford ta saka sunan dan kwallon a cikin 'yan wasan da za ta rage, kafin Arsenal ta ganshi ta kuma yi sha'awarsa.