Kungiyar Liverpool ta saka Mamadou Sakho a kasuwa

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rabonda Sakho ya buga wa Liverpool wasanni tun cikin watan Afirilun da ya wuce

Kungiyar Liverpool ta ce za ta sallamar da Mamadou Sakho kan kudi fam miliyan 20 ga duk kulob din da ke son daukar dan wasan a cikin watan Janairun nan.

Galatasaray da Sevilla sun nuna sha'awar sayen dan wasan mai shekara 26, ita ma Southampton na son sayan dan kwallon Faransa, bayan da ta ce kyaftin dinta Jose Fonte zai iya barinta a bana.

A shekarar 2015 ne Sakho ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Anfield zuwa shekaru da dama.

Sai dai kuma rabon da dan kwallon ya buga wa Liverpool tamaula tun cikin watan Afirilun da ya wuce, bisa wasu dalilai da kungiyar ta yanke.

Sakho ya buga wa Liverpool wasannin League 56 a shekara ukun da ya yi a Anfield, yanzu yana taka-leda a karamar kungiyar ta matasa 'yan kasa da shekara 23.