Manchester United ta sayar da Schneiderlin ga Everton

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Schneiderlin ya koma United a watan Yulin 2015

Manchester United ta sallamar da Morgan Schneiderlin ga Everton kan kudi fan miliyan 22.

Tsohon kociyan United, Louis van Gaal ne ya sayo Schneiderlin daga Southampton kan kudi fam miliyan 25 a watan Yulin 2015.

Dan kwallon ya buga wa United wasanni 47, inda ya yi wasanni takwas a karkashin kociya Jose Mourinho a bana, ciki har da guda uku da ya kara a gasar cin kofin Premier.

Kungiyoyin biyu sun cimma matsaya, bayan kwanaki uku da kociyan Everton Ronald Koeman ya bukaci mahukuntan kulob dinsa da su sayo karin 'yan kwallo a cikin watan Janairu.