Democrat: Dole Trump ya sauya mukamin da ya baiwa surukinsa

Jared Kushner

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dokar hana son kai a ba da aiki ba ta hana Jared Kushner aiki a fadar White House ba, inji lauyarsa

'Yan jam'iyyar Democrat sun yi kira ga zababben shugaban Amurka, Donald Trump, da ya sauya mukamin babban mai ba da shawarar da ya bai wa surukinsa, domin damuwa kan son kai da kuma cin karon muradunsa da na kasa.

Wata kungiya na son ma'aikatar shari'a da kuma ofishin da'a a aikin gwamnati, su binciki lamuran shari'ar da suka jibinci nada Jared Kushner dan shekara 36 a mukamin gwamnati.

Lauyarsa ta ce mukamin da aka bashi bai karya wata dokar hana son kai ba.

Mista Kushner yana auren diyar Trump, Ivanka .

Miloniyan zai sauka daga jagorancin harkar sayar da gidaje da kuma kasancewa shugaban jaridar New York Observer domin bin dokar da'a, inji lauyarsa, Jamie Gorelick.

Ta kara da cewar mai bai wa Trump shawaran zai kuma rage mafi yawan kadarorinsa.

Za'a rantsar da Trump a matsayin shugaban Amurka na 45 ranar 20 ga watan Janairu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ivanka Trump ta auri Jared Kushner a 2009 kuma ma'auratan suna da 'ya'ya uku.

Wasu daga cikin wadanda ya zaba a majalisar ministocinsa, suna da harkokin kasuwanci wadanda za'a bincika a zaman tabbatar da su a wannan makon.

Wanda Mista Trump ya zaba a matsayin Atoni Janar, Sanatan Alabam Jeff Session, shi ne zai fara fuskantar zaman tabbatarwa na majalisar dattawa a ranar Talata.

An ki tabbatar da shi a mukamin alkalin tarayya a 1986 bisa zargin da aka yi masa na kalaman wariyar launin fata.

Amma banda ministoci, ana kallon masu ba da shawara a matsayin ma'aikatan fadar White House kuma basu bukatar yardan majalisar dokoki.

Waye Jared Kushner?

Mista Kushner, wani babban attajiri ne a harkar ginawa da sayar da gidaje da kuma harkar buga jarida, wanda ya taka gagarumar rawa a yakin neman zaben Mista Trump kuma ya halarci muhimman ganawa da shugabannin kasashen waje a lokacin mikawa Trump mulki.

mai magana a hankali kuma wanda ba ya son fitowa a kafafen watsa labarai,

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Cikin wannan gidan da ke unguwar Kalaroma ta Washington DC ne Ivanka Trump da Jared Kushner za su zauna.

Mabiyin masharuriyar darikar yahudawa wanda kakanninsa suka tsira daga kisan kare-dangin Holocaust, ya girma a Livingston a jihar New Jersey kuma ya karanci halayyar zaman jama'a a jami'ar Havard.

Babansa, wani attajiri a harkar gidaje, an daure shi kan laifin kin biyan haraji, bada gudumawar kudin yakin neman zabe ba bisa ka'ida ba da kuma yin katsalandan kan shaida a 2005.