An zabi tsohon shugaban 'yan tawaye a matsayin kakakin majalisar Ivory Coast

Guillaume Soro

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Guillaume Soro (tsakiya) ake ganin zai gaji Shugaba Alassane Ouattara

An zabi tsohon shugaban 'yan tawaye kuma tsohon firayi ministan Ivory Coast, Guillaume Soro, a matsayin kakakin majalisar dokokin kasar da gagarumin rinjaye, inda kashi 95 cikin 100 na 'yan majalisa suka zabe shi.

An tabbatar da Mista Soro a mukaminsa ne jim kadan bayan Shugaba Alassane Ouattara ya sallami shugabannin hukumomin tsaro na kasar bayan boren da ya girgiza barikokin soji a makon jiya.

Ya tsaya a zaben ne a matsayin dan majalisar indipenda inda ya yi takara da Evariste Meambly, dan takaran jami'iyyar RHDP mai mulki.

Mista Soro ya bayyana cewa zaman majalisar na farko da zai jagoranta yau zai karbi bakuncin Shugaba Ouattara, wanda ake sa ran zai ayyana wanda ya zaba a matsayin mataimakin shugaban kasa a karkashin sabon tsarin mulki.

Ana ganin kakakin majalisar a msatyin wanda zai gaji Shugaba Ouattara a lokacin da zai sauka daga karagar mulki a shekarar 2020 a karshen wa'adinsa na biyu.