An lalata mutum-mutumin Messi a Argentina

Argentina

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ba a san dalilan da ya sa aka lalata batun batumin Messi ba

An lalata mutum-mutumin fitaccen dan wasan Argentina, Lionel Messi a birnin Buenos Aires.

Wadanda suka yi aika-aikar sun raba mutum-mutumin gida biyu, inda aka cire kai da hannuwa.

A watan Yunin da ya wuce ne aka kaddamar da mutum-mutumin dan kwallon wanda aka kera da azurfa.

Ba a dai san dalilan da suka sa aka lalata mutum-mutumin ba, amma mahukunta sun ce sun fara gyara abubuwan da aka lalata.

Asalin hoton, LA NACION TWITTER

Bayanan hoto,

Jaridar La Nacional ce ta watsa labarin a kafarta ta twitter

An kuma kera mutum-mutumin ne a lokacin da Messi ya sanar da yin ritayar buga wa Argentina tamaula... daga baya ne ya sauya shawara bayan an yi ta rokonsa.

An kafa mutum-mutumin Messi a kan titin Paseo de la Gloria a wurin da ake ajiye fitattun 'yan wasan kasar da suka taka rawa ciki har da Gabriela Sabatini dan kwallon tennis da Manuel Ginobili mai wasan kwallon kwando.