Man United ta doke Hull a gasar League Cup

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar 26 ga watan Janairu ne United za ta ziyarci Hull City

Manchester United ta samu nasara a kan Hull City da ci 2-0 a gasar League Cup wasan farko na daf da karshe da suka kara a ranar Talata.

United ta ci kwallon farko ta hannun Juan Mata a Old Trafford, bayan da ya samu tamaula daga bugun da Henrikh Mkhitaryan ya saka wa kai.

Marouane Fellaini ne ya ci ta biyu da kai, bayan da shi kuma ya samu kwallo daga bugun da Matteo Darmian ya yi wo.

Manchester United za ta ziyarci Hull City a wasa na biyu na daf da karshe a gasar League Cup a ranar 26 ga watan Janairu.

A ranar Laraba ne Southampton za ta karbi bakuncin Liverpool a daya wasan farko na daf da karshe a gasar ta League Cup.