Madrid za ta ziyarci Sevilla a Copa del Rey

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ce ke mataki na daya a kan teburin La Liga

Real Madrid ta bayyana 'yan wasa 19 da su kara da Sevilla a wasa na biyu na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar Copa del Rey da za su yi a ranar Laraba.

Madrid wadda ke matsayi na daya a kan teburin La Liga ta doke Sevilla 3-0 a wasan farko da suka yi a Santiago Bernabeu a ranar 4 ga watan Janairu.

Real ta ci kwallayenta uku ta hannun James Rodriguez wanda ya zura biyu a raga daya a bugun fenariti da kuma wadda Raphael Varane ya ci.

Madrid ta yi wasanni 39 a jere ba tare da an doke ta ba, wanda hakan ya sa ta yi kan-kan-kan da Barcelona wadda ta kafa tarihin yawan lashe wasannin a kakar bara.

Tuni kuma Real Madrid ta sanar da 'yan wasan da za su buga mata wasan.

Masu tsaron raga: Keylor Navas, Casilla da kuma Yáñez.

Masu tsaron baya: Carvajal, Ramos, Varane, Nacho, Marcelo, Coentrao da kuma Danilo.

Masu wasan tsakiya: Kroos, Casemiro, Kovacic, Asensio da kuma Enzo.

Masu cin kwakko: Benzema, Lucas Vázquez, Mariano da kuma Morata.