Everton na son daukar Ishak Belfodil

Cup of nations Gabon 2017

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Algeria ba ta gayyaci Belfodi gasar cin kofin nahiyar Afirka ba

Everton ta tuntubi Standard Liege domin sanin ko za a sayar mata da Ishak Belfodi wanda aka yi masa farashi fam miliyan 10.

Daraktan wasanni na Everton, Steve Walsh, ya ce Belfodi dan kwallon Algeria mai shekara 24 dan kwallon Algeria zai dace da Everton da irin salon wasan da yake yi.

Everton na kokarin sayo karin 'yan kwallo, bayan da koci Ronald Koeman ya bukaci hakan tun lokacin da Leicester ta fitar da ita daga gasar cin kofin FA.

Tuni dan kwallon Manchester United, Morgan Schneiderling ya isa Goodison Park domin a duba lafiyarsa a shirin da yake yi na komawa can da murza-leda.

Tuni Everton ta dauko dan kwallon Charlton Athletic Ademola Lookman kan kudi fam miliyan 11 a cikin watan Janairu.