Makalele ya zama mataimakin kocin Swansea

Swansea City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Paul da Makalele a lokacin da suka yi aiki a Paris St-Germain

Swansea City ta nada tsohon dan wasan Faransa da Chelsea, Claude Makelele, a matsayin mataimakin koci kan yarjejeniyar kakar wasa daya.

Makelele zai taimakawa Paul Clement aiki, wanda suka taka-leda tare a Chelsea a 2007 zuwa 2008, zai kuma halarci karawar da kungiyar za ta yi da Arsenal a gasar Premier a ranar Asabar.

Tsohon dan wasan Faransa wanda ya yi mata kwallo sau 71, ya lashe kofuna 15 ciki har da guda biyu a gasar Premier a Chelsea da na zakarun Turai da ya dauka a Real Madrid a 2002.

Bayan da ya yi ritaya ne aka nada shi koci a PSG, daga nan ya jagoranci Basia wata shida, sannan ya koma daraktan wasanni na Monaco.