Miura zai ci gaba da wasa yana da shekara 50

Japan League

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Miura ya ci kwallo biyu a wasanni 20 da ya buga a gasar da ta wuce

Tsohon dan kwallon tawagar Japan, Kazuyoshi Miura, zai ci gaba da buga wa Yokohama tamaula yana da shekara 50.

Miura, wanda ya yi ritaya daga buga wa Japan tamaula shekaru 17 da suka wuce, shi ne dattijon da ya ci kwallo yana da shekara 49 a gasar bara.

A watan Fabrairu mai kamawa Miura zai cika shekara 50 da haihuwa, a kuma lokacin ne za a fara gasar cin kofin Japan.

Dattijon wanda ya murza-leda a nahiyar Turai, ya ci wa Japan kwallaye 55 a wasanni 89 da ya buga mata kafin ya yi ritaya.

Miura ya fara wasa a kungiyar Santos ta Brazil a kwararren dan kwallo a 1986, ya kuma taka-leda a Genoa da Dinamo Zagreb a shekarar 1990.

Ya koma Yokohama a 2005 yana da shekara 38, kuma a lokacin shi ne dattijon da ke murza-leda wanda daga baya ya je Vissel Kobe.