Southampton ta fara jin kanshin League Cup

English League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Redmon ne ya ci wa Southampton kwallon a karawa da Liverpool

Southampton ta ci Liverpool daya mai ban haushi a wasan farko na daf da karshe a gasar League Cup da suka fafata a ranar Laraba.

Southampton ta ci kwallon ne ta hannun Nathan Redmond a minti na 20 da fara tamaula.

Liverpool za ta karbi bakuncin Southampton a wasa na biyu na gasar cin kofin a ranar Laraba 25 ga watan Janairu.

Kuma a ranar Alhamis ne Manchester United wadda ta ci Hull City 2-0 a gasar ta League Cup ranar Talata za su yi wasansu na biyu.