Fellaini zai ci gaba da wasa a United zuwa kakar 2018

Manchester United

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Fellaini ya yi wa United wasanni 21 a kakar wasan bana

Manchester United ta tsawaita yarjejeniyar ta da Maroune Fellaini domin ya ci gaba da wasa a Old Trafford har zuwa karar wasan 2018.

Fellaini ya saka hannu kan kwantiragin shekara hudu a United a shekarar 2013, tare da yarjejeniyar tsawaita ta shekara daya a lokacin da ta dauko shi daga Everton kan kudi fam miliyan 27.5.

Kociyan United, Jose Mourinho ne ya amince a kara wa dan kwallon shekara daya kan yarjejeniyar baya, duk da cewar dan wasan mai shekara 29 ba ya taka rawar gani a wasanninsa.

A watan jiya ne magoya bayan Everton suka yi wa Fellaini ihu, sai dai kuma shi ne ya ci kwallo na biyu da United ta doke Hull City 2-0 a gasar League Cup a ranar Talata.

Yana kuma cin kwallo ya ruga a guje ya rungumi Mourinho domin ya ta ya shi murnar kwazon da ya yi, duk da cewar shi ne ya jawo fenaritin da Everton ta ci United a ranar 4 ga watan Disamba.