Ma'aikatan mai sun soma yajin-aiki a Nigeria

Masu tayar da kayar baya sun fasa bututan mai a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu tayar da kayar baya sun fasa bututan mai a Najeriya

Kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas ta soma yajin gama-gari saboda korar 'ya'yanta daga aiki da ake yi.

Kakakin kungiyar PENGASSAN, Emmanuel Ojugbana, wanda ya shaida wa BBC hakan, ya kara da cewa sun dauki matakin ne saboda kamfanonin man da suke yi wa aiki ba sa aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla kan jin dadin ma'aikata.

A cewarsa, za su tattauna da ministan kwadagon kasar Chris Ngige domin ya shiga tsakaninsu da kamfanonin man.

Yajin-aikin dai zai yi tasiri wajen hako da fitar da man fetur da iskar gas.

Kungiyoyin ma'aikatan man dai sun dade suna yajin-aiki a Najeriya, akasari domin su matsa a aiwatar da wasu matakai da suke son ganin an dauka.

Sai dai 'yan kasar da dama na ganin yajin-aiki ba shi ne mafita ba.