Chelsea ta samu amincewar gina sabon filin wasa

Sabon filin Chelsea
Bayanan hoto,

Sabon filin da Chelsea za ta gina zai dauki 'yan kallo 60,000

An amince wa kungiyar Chelsea ta gina sabon filin wasa mai cin 'yan kallo 60,000 a kan kudi fam miliyan 500.

Kwamitin tsare-tsare na karamar hukumar Hammersmith da na Fulham ne suka marawa shirin baya, kuma kungiyar za ta rusa filinta na Stamford Bridge mai daukar 'yan kallo 41,600.

Chelsea ta ce "Amincewar da kwamitin ya yi ba yana nufin fara aikin ginin ba ne nan take, illa dai muhimmin abu ne da ya kamata mu bi, kafin mu samu amincewar".

Magajin garin Landan, Sadiq Khan ne zai bai wa Chelsea umarnin karshe don gina filin wasan ko kuma a'a.

Herzog da De-Meuron wadanda suka gina Olympic stadium ta Beijing da ake kira da shekar tsuntsu, su aka bai wa kwangilar gina sabon filin wasan na Chelsea.

Kuma wannan matakin na nufin Roman Abramovich sai ya nemi izinin wani filin da Chelsea za ta koma buga wasanninta tsawon shekara uku.

Tuni kuma Chelsea ta rubuta takardar neman izinin koma wa filin wasa na Twickenham da Wembley.