Benteke ba na sayarwa ba ne — Allardyce

Crystal Palace

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Benteke ya ci kwallaye takwas a kakar wasan bana

Kociyan Crystal Palace, Sam Allardyce, ya ce ba za su sayar da Christian Benteke ba, domin yana bayar da gudunmawa a kungiyar.

Benteke, mai shekara 26, ya koma Palace ne a watan Agustan da ya wuce kan kudi fam miliyan 27 daga Liverpool.

Sai dai kuma ana ta rade-radin cewar dan kwallon zai bar Palace, bayan da kungiyar ba ta taka rawar ganin a gasar bana.

Dan wasan na Belgium ya ci kwallaye takwas a kakar bana, sai dai kuma ya yi wasanni biyar a jere ba tare da ya ci kwallo ba.

Crystal Palace tana matsayi na 17 a kan teburin Premier.