Real Madrid ta buga wasa 40 ba tare da an doke ta ba

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ce ta daya a kan teburin La Liga

Real Madrid ta kafa sabon tarihi na kasancewa kungiyar da ta buga wasa sau 40 a Spain ba tare da an doke ta ba yayin da kwallon da Karim Benzema ya zura a minti na 93 ta yi sanadin tashin su 3-3 da Sevilla a rukunin 'yan 16 na gasar cin kofin Copa del Rey.

A watan Afrilun da ya wuce ne Madrid ta sha kashi a hannun Sevilla a matakin dab da na kusa da na karshe, wato kwata-fainal a gasar cin kofin Zakarun turai.

A baya dai Barcelona ta kafa tarihin zama kungiyar da ba a doke ta ba a wasanni 39 a jere, tsakanin shekarar 2015 da 2016 a karkashin jagorancin Luis Enrique.

Wasan da Real ta yi na ranar Alhamis na nufin yanzu ta kai matakin kwata-fainal a gasar ta Copa del Rey.

An nada tsohon dan wasan Juventus da Real da kuma Faransa Zidane, mai shekara 44, a matsayin kocin kungiyar ne a watan Janairu na shekarar 2016.

Nasarar da yake samu a wasannin da ya jagoranta ta fi kayen da ya sha domin kuwa ya ci gasar zakarun Turai, da ta kwallon kafar duniya na kulob-kulob da kuma ta Uefa Super Cup, yayin da ya sha kashi sau biyu.

Real ta ci wasanni 31 sannan ta yi kunnen-doki a wasanni tara tun dokewar da aka yi mata ta karshe, don haka ta ci kwallaye 115 sannan ta zubar da 39.

Barcelona kuma ta yi nasara a wasanni 32 sannan ta yi kunnen-doki a wasanni bakwai a dukkanin gasar da ta buga tsakanin watan Oktoba na shekarar 2015 zuwa watan Maris na 2016.

A wasan na ranar Alhamis dai, Sevilla ta doshi yin nasara amma Benzema da Marcelo sun yi wasa da kwallo a tsakiyar fili, sannan Benzema din ya soka kwallon da ta ba su nasara.

Sevella ta fara yin nasara ne bayan dan wasan Real Danilo ya ci kan su, koda yake Marco Asensio ya fanshe.

Sai dai kwallon da Stevan Jovetic ya zura ta sanya Sevilla fatan cewa ita ce za ta yi nasara.

Amma Sergio Ramos ya zura kwallo a minti na 83, sannan Benzema ya zura kwallo ta karshe lamarin da ya sa suka tashi 3-3.

Mun gyara kura-kuran da kuka gani a wannan labari tun da farko, kuma muna neman afuwa. Mun gode