Madrid za ta kara da Celta a Copa del Rey

Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ta kafa tarihin buga wasanni 40 ba tare da an doke ta ba.

Real Madrid za ta fafata da Celta Vigo a wasan daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey.

Madrid ta kai wannan matakin ne bayan da ta ci Sevilla 6-3 a wasanni biyu da suka yi, yayin da Celta ta ci Valencia 6-2.

Mai rike da kofin bara, Barcelona, za ta kece raini da Real Sociedad, ita kuwa Atletico Madrid za ta kara ne da Eibar.

Kungiyar Alcorcon wadda ita kadai ce ba ta buga wasannin La ligar Spaniya za ta yi gumurzu ne da Deportivo Alaves.

Barcelona ce a kan gaba wajen yawan lashe Copa del Rey, bayan da ta dauki 28, sai Athletic de Bilbao mai 23, Real Madrid kuwa 19 ne da ita da Atletico de Madrid mai guda 10 a tarihi.

Za a fara wasannin farko a gasar daf da na kusa da karshe a ranar 18 ga watan Janairu, sannan a yi karon batta a karo na biyu a ranar 25 ga watan Janairun 2017.

Ga jadawalin wasannin da za a yi:

  • Real Sociedad da Barcelona
  • Alcorcon da Alaves
  • Atletico Madrid da Eibar
  • Real Madrid da Celta