'Yan wasan Jamhuriyar Congo sun ki zuwa atisaye

Gasar cin kofin nahiyar Afirka
Bayanan hoto,

A ranar Litinin Jamhuriyar Congo za ta fafata da Morocco

Yayin da za a bude gasar cin kofin Afirka a ranar Asabar wanda Gabon ke karbar bakunci a bana, 'yan wasan Jamhuriyar Congo sun ki zuwa atisaye.

'Yan wasan na Jamhuriyar Congo na yin yajin aiki ne kan rage musu kudin fafatawar da za su yi a Gabon, da kuma kasa biyansu bashin da suke bi na gasar da aka yi a 2015.

Jamhuriyar Congo wadda ke rukuni na uku, za ta buga wasan farko a gasar kofin Afirka a ranar Litinin da Morocco.

Tawagar ta Jamhuriyar Congo ta kai wasan daf da karshe a gasar da aka yi a Equatorial Guinea daga nan ta kare a mataki na uku a wasannin da aka yi a 2015.