Filin wasa na Kano ya cika da 'yan kallo

Gasar Firimiyar Nigeria
Bayanan hoto,

Bikin fara gasar Firimiyar Nigeria a karawa tsakanin Kano Pillars da Ifeanyiubah a jihar Kano, Nigeria

Filin wasa na Sani Abacha da ke Kano ya cika makil - babu masakar tsinke - amma komai na tafiya lami-lafiya.

Akwai jami'an tsaro da dama a filin da kewayensa domin tabbatar da tsaro a wasan.

Cikin manyan bakin da suka halarci wasan kungiyar, har da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da wasu manyan jami'an hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya.

A kakar bara Kano Pillars ce ta doke Ifeanyi Ubah a filin wasan na Sani Abacha da ke jihar Kano