Arsenal ta koma ta uku a kan teburin Premier

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Olivier Giroud ya ci wa Arsenal kwallaye 13

Arsenal ta koma cikin 'yan hudun farko a kan teburin gasar Premier, bayan da ta ci Swansea 4-0 a wasan mako na 21 na gasar da suka fafata a ranar Asabar.

Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun Olivier Giroud tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a karawar da Swansea ta karbi bakuncin fafatawar.

Bayan da aka dawo daga hutu ne 'yan kwallon Swansea Jack Cork da kuma Kyle Naughton suka ci gida, daga baya kuma Alexis Sanchez ya ci ta hudu a wasan.

Da wannan sakamakon Arsenal ta hada maki 44 a wasanni 21 da ta buga ta kuma koma mataki na uku a kan teburin na Premier.

Arsenal za ta buga wasan gaba da Burnley, yayin da Swansea City za ta ziyarci Liverpool.