Kofin Afirka: Gabon da Guinea-Bissau sun raba maki

Gasar cin kofin Afirka Hakkin mallakar hoto Gebriel Bouys
Image caption Wanan ne karon farko da Guine-Bissau ke buga gasar cin kofin nahiyar Afirka

Mai masaukin bakin gasar cin kofin nahiyar Afirka, Gabon ta raba maki da Guinea-Bissau, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a wasan da suka yi a ranar Asabar.

Gabon ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasanta mai taka-leda a Borussia Dortmund Pierre-Emerick Aubameyang minti na biyar da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

Guinea-Bissau wadda wannan ne karon farko da fara shiga gasar kofin nahiyar Afirka ta farke ne ta hannun Juary Soares.

Gabon za ta buga wasa na biyu na cikin rukunin farko da Burkina Faso a ranar 18 ga watan Janairu, kuma a ranar ne Kamaru za ta kece raini da Guinea-Bissau.

Labarai masu alaka