Everton ta ci mutuncin Manchester City

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Everton tana mataki na bakwai a kan teburin Premier, bayan wasanni 21 da ta buga a gasar

Everton ta tozarta Manchester City a gasar Premier, bayan da ta doke ta da ci 4-0 a wasan mako na 21 na gasar da suka fafata a Goodison Park a ranar Lahadi.

Everton ta fara cin kwallo ta hannun Romelu Lukaku saura minti 11 a je hutun rabin lokaci, kuma hakan aka tafi hutun Everton da kwallo daya a ragar City.

Bayan da aka dawo ne daga hutun Everton ta kara cin kwallaye uku ta hannun Kevin Mirallas da Tom Davies da kuma Ademola Lookman wanda ya ci tashi aka kuma kammala karawar.

Da wannan sakamakon Everton ta hada maki 33 tana kuma mataki na bakwai a kan teburi, yayin da Manchester City ke matsayi na biyar da maki 42 a gasar Premier ta bana.

Everton za ta ziyarci Crystal Palace a wasan mako na 22 a ranar Asabar, a kuma ranar ce Manchester City za ta karbi bakuncin Tottenham a Ettihad.