Dambe takwas aka yi, hudu babu kisa, Arewa da Kudu suka yi nasara a wasanni bibiyu

Dambe takwas aka yi, hudu babu kisa, Arewa da Kudu suka yi nasara a wasanni bibiyu

Wasanni takwas aka dambata a Abuja a ranar Lahadi, guda hudu daga ciki aka tashi babu kisa, Kudu da Arewa suka yi nasara a karawa bibiyu.

Cikin dambatawa takwas din da aka yi, Kuduwa sun yi kisa a wasanni biyu, yayin da bangaren Arewa ma suka samu nasara a fafatawa biyu, sannan aka tashi babu kisa a karawa hudu.

Wasannin da Kudawa suka yi nasara sun hada da gumurzun da Dogon Dan Polis ya buge Shagon Bahagon Na Bacirawa da wanda Shagon Bahagon Bala ya doke Hussaini.

Nasarorin da Arewa suka samu sun hada da wanda Shagon Lawwalin Gusau ya buge Shagon Bahagon Gurgu da kuma wasan da Shagon Garba Dan Malumfashi ya kai Shagon Dan Matawalle kasa.

Wasannin da aka tashi babu kisa kuwa:

Shagon Dan Polis daga Kudu da Na Bacirawa Karami daga Arewa

Aminun Mahaukaci Teacher daga Arewa da Sanin Shagon Kwarkwada daga Kudu

Dan Aliyu Langa-Langa daga Arewa da Bala Shagon Kwarkwada daga Kudu

Shagon Fatalwa daga Kudu da Shagon Bahagon Maru daga Arewa

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton