Bayern Munich ta dauki Rudy da Sule

Bundesliga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan da Bayern Munich ta kulla yarjejeniya da su Rudy da Sule, wadanda za su taka-mata leda a kakar wasanni ta badi

Bayern Munich ta kulla yarjejeniya da 'yan wasan Hoffenheim, Sebastian Rudy da kuma Niklas Sule, domin su buga mata tamaula.

'Yan wasan biyu za su ci gaba da taka-leda a Hoffenheim wadda take ta biyar a kan teburin Bundesliga har zuwa karshen kakar bana.

Sule mai tsaron baya ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, yayin da Rudy wanda kwantiraginsa za ta kare a Hoffenheim a karshen wasannin bana, zai yi shekara uku a Munich.

A ranar Juma'a ne za a ci gaba da wasannin gasar cin Kofin Bundesliga bayan hutun Kirsimeti, a kuma ranar ce Munich za ta ziyarci Freiburg.

Bayern Munich tana matsayi na daya a kan teburin Bundesliga, inda ta bayar da tazarar maki uku tsakaninta da RB Leipzig wadda ke mataki na biyu.