Man United da Liverpool sun raba maki a Premier

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United tana mataki na shida a kan teburi, ita kuwa Liverpool tana matsayi na uku.

Manchester United ta raba maki da Liverpool, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a wasan mako na 21 a gasar Premier da suka yi a ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara cin kwallo a bugun fenariti ta hannun James Milner, bayan da Paul Pogba ya taba tamaula da hannu a cikin da'ira ta 18 din United.

United ta farke ta hannun Zlatan Ibrahimovic saura minti shida a tashi daga wasan, kuma hakan ya sa dan wasan ya ci kwallaye 14 a bana, ya kuma yi kan-kan-kan da Costa da kuma Sanchez.

Da kuma wannan sakamakon United tana mataki na shida a kan teburi da maki 40, ita kuwa Liverpool tana matsayi na uku da maki 45.