Man United ta yi wasanni 16 a jere ba a doke ta ba

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United tana matsayi na shida a kan teburin Premier

Manchester United ta buga wasanni 16 a jere ba tare da an doke ta a gasar Premier da kofin Europa da League Cup a bana.

Rabon da a doke United wadda ke mataki na shida a teburin Premier, tun rashin nasarar da ta yi a gidan Fenerbahce a gasar Europa Cup 2-1 ranar 3 ga watan Nuwamba.

United wadda ta buga kunnen doki da Liverpool a ranar Lahadi a gasar Premier, ta ci wasanni 12 sannan ta buga canjaras a karawa hudu a fafata 16 da ta yi a jere ba a doke ta ba a bana.

A kuma tsawon lokacin United ta ci kwallaye 36, sannan aka zura mata kwallo 9 a ragarta.

United za ta ziyarci Stoke City a wasannin mako na 23 a gasar Premier a ranar 21 ga watan Janairu sannan ta ziyarci Hull City a gasar League Cup ranar 26 ga Janairun.