Robben ya tsawaita zamansa a Bayern Munich

Bayern Munich
Bayanan hoto,

Robben ya koma Munich daga Real Madrid a shekarar 2009

Arjen Robben ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da buga wasa a Bayern Munich zuwa 2018.

A kakar bana kwantiragin Robben tsohon dan wasan Chelsea za ta kare a Munich din, amma yanzu zai ci gaba da wasanni a Jamus har zuwa lokacin da zai kai shekara 34.

Robben ya koma Munich da taka-leda daga Real Madrid kan kudi fam miliyan 24 a shekarar 2009, ya kuma ci wa kungiyar kwallaye 82 a wasanni 152 da ya buga mata.

Haka kuma a cikin kakar wasannin bana Franck Ribery da Robert Lewandowski suka tsawaita yarjejeniyarsu ta zama a Bayern Munich.

A kuma ranar Lahadi Bayern ta sanar da daukar Sebastian Rudy da kuma Niklas Sule daga Hoffenheim.