West Ham ta ki sallamar da Payet ga Marseille

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Payet ya ci wa West Ham kwallaye biyar a wasannin bana

West Ham United ta ki ta sallama tayi na biyu da Marseille ta yi wa dan kwallon tawagar Faransa Dimitri Payet.

Tun farko Marseille ta taya Payet kan kudi fam miliyan 19, sannan ta kara fam miliyan daya a kan tayin farko, inda shugaban kungiyar West Ham, David Sullivan, ya ce ba za su sayar da dan wasan ba.

Kociyan West Ham United, Slaven Bilic, ya sanar a baya cewar Payet ya ce baya sha'awar ya ci gaba da buga wa kungiyar tamaula.

A yanzu haka dan kwallon mai shekara 29 ya koma taka-leda a karamar kungiyar West Ham ta 'yan wasa masu shekara 23.

West Ham mai buga gasar Premier ta ce a shirye take Payet ya nemi afuwa ga magoya bayan kungiyar sannan ya koma yin atisaye.