Costa ya yi atisaye shi kadai a Chelsea

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Costa ya ci wa Chelsea kwallaye 14 a gasar Premier ta bana

Dan wasan Chelsea, Diego Costa, ya yi atisaye shi kadai a rana ta biyu a filinta na Cobham.

Dan kwallon bai buga wa kungiyar wasan Premier da ta ci Leicester a ranar Asabar ba, sakamakon ciwon baya da yake fama da shi kamar yadda koci Antonio Conte ya sanar.

Rahotanni na cewa Costa da Conte sun samu rashin jituwa a tsakaninsu, har ma ana cewa dan kwallon tawagar Spaniya zai koma taka-leda a gasar China ne.

Costa wanda ya ci kwallaye 14 a wasanni 19 da ya buga wa Chelsea a bana, bai buga atisayen kwanaki uku a makon jiya ba, za kuma a duba lafiyarsa a ranar Talata domin fayyace idan zai iya motsa jiki tare da 'yan kwallon Chelsea.

Kungiyar wadda take mataki na daya a kan teburin Premier za ta karbi bakuncin Hull City a wasannin mako na 22 na gasar.