United ta tsawaita zaman Valencia a Old Trafford

Gasar Premier
Bayanan hoto,

Antonio Valencia ya ci wa United kwallaye 13 a gasar Premier

Manchester United ta tsawaita yarjejeniyar Antonio Valencia domin ya ci gaba da murza-leda a kungiyar zuwa 2018.

United ta sayi Valencia dan kasar Ecuador mai shekara 31, mai buga wasan gefe daga Wigan a shekara 2009.

Daga baya ne kungiyar ta mayar da shi mai tsaron baya a lokacin Louis van Gaal, kafin nan Sir Alex Ferguson ya yi amfani da shi a wannan gurbin jifa-jifa.

A makon jiya ne United ta tsawaita yarjejeniyar Marouane Fellaini, wanda zai ci gaba da taka-leda zuwa karshen kakar wasan badi.

United tana mataki na shida a kan teburin Premier da maki 40, inda za ta fafata a wasan mako na 22 da Stoke City.