Ranieri na fatan Conte ya lashe kofin Premier bana

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea tana matsayi na daya a kan teburin Premier, yayin da Leicester ke mataki na 15

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri na son Antonio Conte ya lashe kofin Premier na bana tare da Chelsea wadda ke matsayi na daya a gasar bana.

Ranieri ya jagoranci Leicester City wadda ta lashe kofin bara a wani abu na almara, amma a bana kungiyar tana matsayi na 15 bayan da ta buga wasannin mako na 21.

Ranieri ya ce "A matsayina na tsohon kociyan Chelsea kuma mai goyon bayan Italiya, ina fatan Conte zai yi nasara".

Ranieri wanda yarjejeniyarsa da Leicester City za ta kare a 2020, ya ce makomarsa a kungiyar ba tabbas duk da taka rawar gani da ya yi a bara.