Costa ya yi atisaye a cikin 'yan wasan Chelsea

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Costa ya ci kwallaye 14 a gasar Premier ta bana

Diego Costa ya yi atisaye tare da 'yan wasan Chelsea a ranar Talata, bayan da ake rade-radin cewar zai koma China da murza-leda.

Dan wasan dan kasar Spaniya ya yi atisaye shi kadai a ranar Litinin, koda yake ya yi hakan ne a tsarin da aka shirya masa domin ya murmure daga jinya da ya yi.

Costa bai buga karawar da Chelsea ta doke Leicester City a gasar Premier a ranar Asabar ba, inda koci Conte ya ce dan kwallon na fama da ciwon baya ne.

Atisayen da Costa ya fara yi tare da 'yan wasan Chelsea na nufin zai iya buga karawar mako na 22 da kungiyar za ta ziyarci Hull City a ranar Asabar a gasar Premier.

Chelsea ce ke mataki na daya a kan teburin Premier da maki 52.