FA ta ci tarar Bacary Sagna

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanya ya yi wa City wasanni 15 a kakar bana

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar Bacary Sagna fam 40,000, bayan dan kwallon ya wallafa jawabi a shafinsa na Instagram cewa alkalin wasa ya ha'ince su.

Dan wasan na Faransa mai shekara 33, ya yi jawabin ne bayan da Manchester City ta ci Burnley 2-1 a gasar Premier a ranar 2 ga watan Janairu.

A karawar alkalin wasa Lee Mason ya bai wa dan kwallon City, Fernandinho jan kati, inda suka karasa fafatawar da 'yan wasa 10 a cikin fili.

Hukumar ta FA ta ce jawabin da dan wasan ya yi tamkar yin fito-na-fito ne da alkalin wasan da ya jagoranci fafatawar, saboda haka ta gargade shi da kada ya kara aikata laifin irin wannan.

Watakila Manchester City ta daukaka kara kan tarar da aka ci dan kwallon.