Toure ya ki amsa tayi mai tsoka daga China

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Toure ya buga wa City wasanni 12 a bana, inda ya ci kwallaye 4

Dan kwallon Manchester City, Yaya Toure, ya yi biris da tayin fam 430,000 da wani kulob ya ce zai dinga ba shi a duk mako.

Kungiyoyin China na son daukar Toure mai shekara 33, tun bayan da ya samu rashin jituwa tsakaninsa da Pep Guardiola kociyan Manchester City.

A karshen kakar wasannin bana ne yarjejeniyar Toure za ta kare a Manchester City.

A cikin watan Nuwamba ne dan wasan ya koma buga wa City wasanni, bayan da suka daidaita da kocin, har ma ya buga wasanni bakwai ya zuwa yanzu.

Bisa doka, Toure zai iya sa hannu don buga wa wata kungiyar waje wasanni a cikin watan Janairu, amma dan kwallon ya gwammace ya ci gaba da buga tamaula a Ingila.

Sai dai kuma har yanzu Guardiola bai fayyace ko zai tsawaita zaman Toure a Ettihad ba.