Madrid za ta karbi bakuncin Celta a Copa del Rey

Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Real Madrid za ta karbi bakuncin Celta de Vigo a wasan farko a Copa del Rey a karawar daf da na kusa da karshe a ranar Laraba.

Shekara biyar kenan rabon da a doke Madrid a Bernabue a wasannin daf da na kusa da karshen, tun bayan nasarar da Barcelona ta yi 2-1 a kanta a ranar 18 ga watan Janairun 2012.

Tun daga lokacin ne Madrid ta ci wasanni 10 ta kuma yi canjaras a karawa biyu a gasar ta Copa del Rey.

Cikin kungiyoyi goma da kungiyar ta doke sun hada da Celta da Valencia da Olímpic de Xàtiva da Osasuna da Espanyol da Atletico Madrid da Cornellà da Cultural da Leonesa da kuma Sevilla.

Wadan da Madrid din ta yi canjaras da su sune Barcelona da kuma Atletico Madrid.

Haka kuma a wasa na biyu ne Alcorcon za ta fafata da Deportivo Alaves.