Everton ta ki bai wa Milan aron Deulofeu

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Everton ta biya kudin daukar Deulofeu a shekarar 2015

Kungiyar Everton ta ki amincewa da tayin da AC Milan ta bukaci a ba ta aron Gerard Deulofeu domin ya buga mata tamaula zuwa karshen wasannin bana.

Dan kwallon mai shekara 22, ya buga wa Everton wasanni 13 tun komawar Ronald Koeman Godison Park a matsayin kociyan kungiyar.

Watakila dan wasan ya koma Ajax, wadda ke son daukar dan wasan, ita ma Middlesbrough na sha'awar ta dauki Deulofeu a cikin watan Janairun nan.

Dan kasar Spaniya ya koma Everton da taka-leda aro a kakar 2013-14 daga Barcelona, daga baya aka biya kudinsa fam miliyan 4.3 a shekarar 2015.

Everton na son sayen dan kwallon Manchester United, Memphis Depay, a cikin watan Janairu, koda yake watakila dan wasan ya je Lyon ta Faransa.