United ta amince ta sayar wa da Lyon Depay

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A shekarar 2015 Depay ya koma United kan kudi fan miliyan 31

Manchester United ta amince ta sayar wa da Lyon Memphis Depay kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 16.

United ta yadda cewar Lyon ta sayar mata da Depay idan ta bukaci dan kwallon daga baya.

Depay dan wasan tawagar Netherlands mai shekara 22, ya ci kwallaye bakwai a wasanni 53 da ya yi tun lokacin da ya koma United kan kudi fam miliyan 31 daga PSV Eindhoven a shekarar 2015.

Dan kwallon ya buga wa United wasanni takwas a kakar bana, kuma rabon da ya yi wasa tun cikin Oktoba, inda ya buga tamaula ta minti takwas.