Louis van Gaal ya ce bai yi ritaya ba

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Van Gaal ya koma United da horar da tamaula a 2014

Tsohon kociyanManchester United, Louis van Gaal, ya ce bai yi ritaya daga horar da tamaula ba, illa dai yana hutawa ne zuwa wani lokaci.

Van Gaal mai shekara 65, baya aiki tun bayan da Manchester United ta sallame shi daga Old Trafford a cikin watan Mayu.

A ranar Litinin wata jaridar Netherlands De Telegraaf ta wallafa cewar Van Gaal ya yi ritaya daga horar da tamaula, kuma mutuwar surikinsa ce ta sa ya dauki wannan matakin.

Sai dai kociyan ya fada a gidan rediyon Spaniya Cadena Ser, cewar zai iya hakura da aikin koci, amma da sauran lokaci tukunna.

Jaridar ta Netherlands ta kuma ce Van Gaal ya ki karbar aikin horar da Valencia kungiyar da ke buga gasar La Liga.

Van Gaal ya ci kofuna bakwai a kungiyar Ajax da Barcelona da Bayern Munich da kuma AZ daga baya ya koma Manchester United a cikin watan Mayun 2014.