Lobi Stars ta ci Kano Pillars 1-0

Pillars za ta buga wasan mako na uku da Shooting Stars
Lobi Stars ta samu nasara a kan Kano Pillars da ci daya mai ban haushi a wasan mako na biyu a gasar Firimiyar Nigeria da suka fafata a ranar Laraba.
Lobi ta ci kwallon ne ta hannun Solomon Kwambe saura minti shida a je hutun rabin lokaci.
Kano Pillars za ta karbi bakuncin Shooting Stars a wasa na uku a ranar 22 ga watan Janairu, a kuma ranar ce Lobi Stars za ta ziyarci MFM a Legas.
Ga sakamakon sauran wasannin mako na biyu da aka buga:
- Ifeanyiubah 4-0 MFM
- Tornadoes 1-1 ABS FC
- Akwa Utd 1-1 Rivers Utd
- Nasarawa 1-1 Rangers
- Abia Warriors 2-0 Katsina Utd
- Gombe Utd 2-1 Remo Stars
- Plateau Utd 3-1 Enyimba
- Sunshine Stars 1-0 3SC