An yi wa Tevez tarbar girma a China

Gasar China
Bayanan hoto,

Tevez ya taka-leda a Manchester City

Daruruwan magoya bayan kungiyar Shanghai Shenua ne suka tarbi Carlos Tevez a filin jirgin sama a China a ranar Alhamis.

Za a gabatar da dan wasan tawagar Argentina mai shekara 32, wanda aka saya fam miliyan 40 daga Boca Juniors a gaban magoya bayan kungiyar a filin wasa na Hongkou.

Tevez zai karbi rarar albashin fam 310,000 a duk mako a gasar ta China, wanda hakan zai sa ya zama dan kwallon kafa da ya fi karbar albashi mai tsoka a duniya.

Magoya bayan Shanghai Shenua sun yi ta kiran sunan "carlos! Carlos a lokacin da aka ratsa da shi cikin dandazon jama'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yadda magoya bayan Shanghai Shenua suka yi ta jiran zuwan Carlos Tevez

Bayanan hoto,

Tevez dan wasan tawagar kwallon kafa ta Argentina

Bayanan hoto,

Yadda magoya baya suke son ganin Tevez a filin jirgin sama