Arsenal ta tsawaita zaman Mertesacker a kungiyar

Gasar Premier

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Mertesacker ya buga wa Arsenal wasanni 24 a kakar badi

Mai tsaron baya na Arsenal, Per Mertesacker, ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da wasa a Gunners zuwa shekara daya.

Dan wasan tawagar Jamus bai buga wa Arsenal tamaula a bana ba, sakamakon rauni da yake yin jinya, wanda ya yi a lokacin atisayen tunkarar wasannin shekarar nana.

A karshen kakar wasannin bana ne yarjejeniyar Mertesacker za ta kare da Arsenal.

Mertesacker ya koma Arsenal da murza-leda daga Werder Bremen a cikin watan Agustan 2011, ya kuma ci kofin FA a kungiyar.

Arsenal tana matsayi na hudu a kan teburin Premier, kuma Chelsea wadda take mataki na daya a kan teburi ta bai wa Gunners tazarar maki takwas.