Barcelona ta ci Sociedad 1-0 a Copa del Rey

Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga

Real Sociedad ta yi rashin nasara a hannun Barcelona a gida a wasan farko na daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey da suka fafata a ranar Alhamis.

Barcelona ta ci kwallon ne tilo ta hannun Neymar Da Silva a bugun fenariti a minti na 21 da fara tamaula.

Daya wasan da aka buga Atletico de Madrid ce ta doke SD Eiber da ci 3-0.

'Yan wasan da suka ci wa Atletico kwallayen sun hada da Antoine Griezmann da Angel Correa da kuma Kevin Gameiro.

SD Eiber da Atletico Madrid za su kara a wasa na biyu a ranar 25 ga watan Janairu, yayin da Barcelona za ta karbi bakuncin Real Sociedad a ranar 26 ga watan na Janairu.