Horon Kyande ya kusa yi wa Dan Kanawa fashin duma

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Turmi biyu suka yi tsakanin Horon Kyande da Shagon Dan Kanawa babu kisa aka raba su

Wasanni 11 aka dambata a gidan damben Ali zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria a ranar Lahadi da safe.

Cikin karawar har da turmi biyu da aka yi tsakanin Horon Kyande daga Arewa da Bahagon Dan Kanawa daga Kudu.

Turmi biyu suka yi babu kisa alkalin wasa Tirabula ya raba su, sai dai a karawar Horon Kyande ya kusa yi wa Bahagon Dan Kanawa fashin duma.

Sai dai kuma Bahagon Horon Kyande daga Arewa buge Shagon Dan Kanawa daga Kudu ya yi a turmin farko, Bahagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu shi kuma ya kai Shagon Bahagon Maru kasa daga Arewa a turmin farko.

Sa zare tsakanin Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu da Shagon Lawwalin Gussau daga Arewa turmi daya suka yi babu kisa.

Sai wasan da Na Bacirawa Karami daga Arewa da ya doke Abbati daga Kudu, haka shi ma Shagon Isuhun Shandam daga Kudu ya buge Shagon Dan Bunza daga Arewa a turmin farko.

Shi kuwa Garkuwan Shagon Dan Malumfashi daga Arewa nasara ya yi a kan Shagon Taye a turmin farko, dambatawa tsakanin Shagon Fanteka daga Kudu da Soja wuta daga Arewa canjaras suka yi.

Karawa tsakanin Bahagon Sunusi Dan Auta daga Arewa da Autan Faya daga Kudu tashi suka yi babu kisa, shi ma damben Dan Shaddadu daga Kudu da Nokiyar Dogon Sani daga Arewa babu wanda ya je kasa.

Daga karshene aka rufe fili da dambatawa tsakanin Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Bahagon Horon Kyande inda suka yi turmi uku babu kisa Tirabula ya raba su.